Friday 2 November 2018

Hausa Novel: Komai Rintsi ( By Hamagee )




馃尫: KOMAI RINTSI馃槍.........


Na 馃尫Hamagee馃尫馃摎


0鈨�1鈨�

    Yarinya yar kimann 4yrs ce  ta saki kuka sakamakon rankwashin da tasha gun wanta,"tashi ki tafi gun uwarki" ya fadi da karfi wanda ya qara kidimar da yarinyar ta tashi da gudu ta nufi side dinsu tana kuka.


  "Me ya sameki Fadwa??"batace komai ba illa sautin kukan da ta qara nan da nan ran momyn ta ya baci dan tasan ba wanda zae sata kuka inba yayyanta ba.Tace "yi shiru ki fada mun, kinyi rashin kunya kou? "Ta gigiza mata kai tace "ya faruk neh ya bugen" sae ta sake fashewa da wani sabon kukan.Wae yarinya qarama har ta san ana mana ba daedae ba, momyn ke fada a ranta ta janyo ta jikin ta tana rarrashin ta "kiyi shiru kinji baby nah zan rama mki"tayi ta lallaminta dae da qyar ta samu tayi shiru har tayi bacci a cinyarta.

 
     Nan momy ta tashi tayi sama da ita, ta kaita dakin ta shimfidata kan gado sannan ta nufi toilet tayi alwala tazo tayi sallahn la'asar ta soma koro adduo'i kan Allah ya raya mata ya da imani sannan Allah ya zabanmata miji na gari ko zataji dadi nan gaba dan gaskya yan uwanta basu sonta ko kadan.Bayan ta idar ta tofa sannan ta tashi ta hau gadon itama,a gefen fadwan ta dan kishingida tana shafa kanta a hankali tana tunani iri*2....


   
    A side din su Ya faruk kuma ummansu tana sauqowa daga sama ta fara fada "wace maciyaciyar yarne ke cikamun kunne da kuka ina bacci?" Tasleem tace "umma wa kuwa banda wancan shegiyar"  (wae kuji yar uwarta take kira shegiya hayan ubansu daya, Allah ya qara mana tsoronshi ya kuma sa mu dace "Ameen").Umman tace "yar iskan yarinya,mema ya kawota nan neh, inta sake zuwa ku mata dukan tsiya nina baku wannan izinin" sannan ta ja tsaki mtswww ta koma daki ta turo qofa da qarfi....n

   Wacece Fadwa da yan uwanta??? Mujee zuwa......nn
[2:54pm, 12/5/2016] Hamagee馃尫: KOMAI RINTSI......馃槍



  By 馃尫Hamagee馃尫馃摎馃摑


0鈨�2鈨�

  Dr. Mahmud Adam sunan mahaifin su fadwa kenan, yanada mata biyu umma wacce itace uwargidansa sae momyn fadwa ce amarya.Iyayen sa wato haj.ameena da alhj.Adam kabeer...Su biyu suka haifa wato shida wansa Barr.Khaleed Adam, sun taso cikin jin dadi da kulawa da juna, iyayensu na matuqar son su da nuna musu tarbiyya, alhj.Adam nada kudi kwarae da gaske,sanaarsa saeda motoci neh, kuma yanada gidajen mai da dama kusan kowane state a Nigeria yanada gidan mai,  hakan yasa yayansa suka taso cikin gata da wadata, sunyi karatunsu na nursery da primary a nan Nigeria sae sukaje London yanda suka qare karatunsu na jamia,Dr.Mahmud ya karanci medcine wanda ya zama consultant shikuma Brr.Khaleed ya karanci law.Tsakaninsu bbu wani nisa a shekaru bae wuce biyu zuwa biyu da rabi ba tsakani kasancewar iyayen basu haihu na fari da wuri ba.wannan kenan


 
   Bayan sun dawo gida neh Barr.Khaleed wato babban dan alhj.Adam ya hadu da yarinya yace yana so me suna Rauda.Rauda yarinya me hankali da nutsuwa gami da tarbiyya ga girmama na gaba, wanda hakan yasa yaji ta kwanta masa a rae, tanada matuqar kyau dan yar niger ce zama neh ya kawo su nan Nigeria ita da iyayenta,am mai transfer neh zuwa nan Yola...


   Baa wani dau lokaci ba soyayya mai qarfi ta shiga tsakanin Khaleed da Rauda har ta kasance manya sun shigo maganar an sanya ranar bikin su.Murna wajen iyayen su baa magana, bayan sunyi aure sae suka koma FCT  wato Abuja da zama amma suna da gida a nan Yolan, gidan amarya yasaha kyau da haduwa ga girma ga kayan alatu kasancewa itama iyayenta masu hali neh daedae gwargwado...


   Bayan bikinsu da shekara guda Allah ya bata ciki ta haifo danta kyakkyawa mai kama da ita aka sa mishi sunan Abba wato Muhammad Adam.Munra wajen dangi da abokan arziqi baa magana, anyi suna mai raeda lfya an watse...

    Dr.Mahmud neh kwance a dakinsa yana waya da Aliya wato umma, wacce suka hadu da ita a london taje karatu,coursemate dinsa ce,  suka qulla soyayyar su.Suna son junan su sosae hatta kai ma yanxu ana maganar aurensu.Bayan biki suma nn birnin tarayyar suka tare suka ci gaba da rayuwar su cikin kwanciyar hankali.Bayan haihuwar su na fari da shekara biyu neh mahaifan su Dr.Mahmud sukayi hatsari suka rasu a hanyarsu ta dawowa daga umra,, Allah ya jiqansu kowa yake cewa, dangi anyi kewarsu har an gode Allah,Mahmud da Khaleed sunyi kukan rashin iyaye ....Bayan anyi zama makokinsu an gama sae akayi rabon gado kowa aka basa nashi..



  KOMAI RINTSI.....馃槍


0鈨�3鈨�
   Bayan shekara 21

    Dr.Mahmud ya tsiri sake yin wani auren wanda shi yyi sanadiyyar samun sabanisa da haj.Aliya,, a yanxu yayansu uku neh babban Adam me shekara 23 sae Tasleem t biyo shi shekarunta 16 da dan dori sae dan auta wato jaleel shikuwa shekarunsa 9 neh....
     Bataso auren ba kou kadan wanda hakn yasa ta tusa yaranta tsanan matar uban.Koda yyi auren sunyi ta azabtar da ita kasancewar uban be cika zama a gida ba,danma momy nada hakuri dan koya dawo bata fada mishi abubuwan da ake mata,, a haka harta haifo yarta kyakyawar gske taci suna Aisha, sunan mahaifiyar momy ce..


     Fadwa ta taso bbu jituwa ko kadan a tsakaninta da yan uwanta,, tsakaninta dsu sai zgi da cin zali...kullum tana gun momyn ta a haka har Allah ya dau ran Dr.Mahmud fadwa nada shekaru uku da watanni ..mutuwarsa ta qara musu zaman takaici kunci, ya rasu ya bar momy da ciki 4mnths.


      Yanzu ya kaiga kou scul zasu saedae akaita da ban amma bazasu tafi da itaba ..kou a scul jaleel bsya so ace ita qanwarsa ce..Yana jss neh yanxu itakuma nursery1 take, bata ma jima da shiga ba dan bayan rasuwan babansu aka sata.Kwanannan faruk ya dawo daga uk yanda ya qare msters dinsa kan geology yanada 27yrs sae Tasleem dake nan apti tana karanta computer science tanada 21yrs.....

     Cigaban labari.....
[2:54pm, 12/5/2016] Hamagee馃尫: KOMAI RINTSI....馃槍


          By
馃尫Hamagee馃尫馃摎馃摑


0鈨�4鈨�
Cigaba da labari...
A haka bacci barawo yyi awon gaba da momy a gefen Fadwa wacce ta jima da yin bacci saedae tana ajiyar zuciya jifa*2..


  Washegari da safe momy ta tashi tayi sallah ta yi musu breakfast sannan ta tada fadwa tayimata wanka itama tayi nata kasancewar yau monday neh momy zata sauqe ta a scul da kanta kwae sae ta wuce gun office dan yaxu ta fara aiki a ministry ov informatn...


   Tana ajiye ta a gate din makarantan sae ga wata yar yarinya itama dae bazata wuce shekarun Fadwan ba,Saeema kenan, qawar tace tare momyn saeeman ta shigar dasu sannan ta komo gun motar momy suka gaesa dan qawartace sunanta haj.Faty,tare sukayi secondary scul da jamia saedae ita bata qare ba kasancewar ita MBBS take, tana auren wani babban mutum dake aiki oil nd gas industrie  yayansu biyu kenan yanxun, Aliyu shine babba yana ss2 neh yanxu sae saeema ta biyun...


    Bayan sun gama yan hiransu sae kowa ta ja mota ta tafi..momy na zaune kan kujeran office dinta wanda yayi kyau iya kyau, yasha furnitures ga air-conditn,system neh a gabanta tana entering wasu documents amma da gani kasan tana cikin damuwa.....


     Shabiyu daedae ta ta fito ta kulle office din ta nufi parking space ta shiga mota ta kama hanyan zuwa daukan Fadwa,,12:23pm daedae ya mata a scul din saeta zauna jiran a tashesu dan 12:30 daman suke tashi kullum in banda fridy da ake tashinsu 12noon...

    Bayan sun tashi sae ta shiga ta daukota snnan suka nufa office din momyn dan daman bata tshi ba sae two take closing.A hanya naga ta staya ta shiga dan wani cafe ta siyo snacks da ice-cream sae youghurt da ruwa sannan suka wuce office din.Koda suka shiga ciki sae momy ta bama Fadwan wani cake da ice-cream 馃崷dan dama mutumin ta kenan,momy kuma ta dau youghurt da meatpie sae shawrma dan ita kyn zaqi basu dameta ba.Sukaci suka sha ruwa  Fadwa tayi ta ma wa momynta tadin uncle dinsu a scul har 2:00pm tayi sannan momy tayi closing ....


   Correction??09020364597 or whatsapp me 08102992472
[2:54pm, 12/5/2016] Hamagee馃尫: *KOMAI RINTSI*......馃槍


  By 馃尫Hamagee馃尫

0鈨�5鈨�
   Suna isowa momy ta danna horn tym din aka bude ta shiga,parking naga tayi sannan ta fito Fadwa na biye da ita sukayi side dinsu suna shiga suka samu da wuta fadwa tazo kunna tv sae momy ta hanata tace sae tayi wanka tayi assingment dinta tukunna _Mommy yau baa bamu home work bafa_ ta fada kaman zatayi kuka, sae momyn tace eh ta bari sae tayi wanka haka ta hakura sanda tayi mata wankan itama tayi sannan ta dauro alwalan sallan laasar dan tayi azahar a office dama.Indomie kawae tayi musu bayan sun gma ci sae ta kunna mata kallon sannan ta wuce daki,,wani akin office ta cigaba da yi a system dinta kafin wayanta ya soma ringing,tana dagawa aka gaida ta ta ansa sannan naji tana cewa _Fadwa na palour tana kallo, ok tou Allah ya kiyaye hanya sae kin dawo_ sannan ta katse wayar..Faiza ce me aikin momy ta kira wayan....
    Karfe uku da minty arbain momy ta tashi tyi sallan laasar sannan ta kunna tvn dakinta tana kallo anan bacci ya dauke ta.Kaman a mafrki ta fara jiyo kukan fadwa aikuwa da sauri ta farka ta fito ko dankwali bbu aknta tana saukowa taga jallel da bulala yana ta tsalama fadwan ita kuma tana kuka ae da gudu tazo ta raba su tana tambayrsa _lfya meyasa yke dukan ta idan ta masa wani abunne bazae zo ya fada mata ba sae dai kwae yyi ta dukan yrinya kamar jakan gidan su_  ran momy be qara baci bama saeda ya fada mata abunda fadwan ta masa, wae uncle dinsu jallel dinne ya tambayeta ta san jaleel neh yaga surename dinsu daya sae tace mai yayanta neh shikuma uncle sae yazo yana tambayan jaleel din dama yana da sister a scul dinnan shine bsu zuwa tare yace mishi ae gidansu ba daya bane....Momy bata san lokacin da tace _shine don rashin imani zakazo kana dukanta ? Fice mun a daki mara mutunci_  yana fita yuuu sae side dinsu ya samu ummansu a daki ta idar da salla kenan tana kan sallayar,kuka ya fashe da umman ta soma tambayar shi meya faru yace _wae dan fadwa ta mun rashin kunya na buge ta shine ta  zazzagen  ta koreni a dakin_  yana kaiwa nan ya cigaba da kuka umma kuwa ta gama quluwa,ta tashi yuuuu sae side din momy tana huci....
    Momy kuwa bayan fitan jaleel ta jawo fadwa jikin ta duk ciwo yana jini ta soma lallaminta zuciyarta na quna saeda ta sake mata wanka ta dan danna mata raunikan da ruwan dumi sannan ta canza mata kaya ta kwantar ita ta tsura mata idanu......
[2:54pm, 12/5/2016] Hamagee馃尫: *KOMAI RINTSI.....馃槍*

By 馃尫Hamageey馃尫

0鈨�6鈨�
   Jin qaran qofa neh ya katse momy da tunanin da takeyi,umma ce ta shigo tana ta ruwan bala'i da masifa _ina kike munafuka ki fito nan_ umma ke fadi.Da jin haka sae momy ta taso ta fito palourn yadda ta taradda umma nata fada tana jijjiga jiki da alaman dae jiran momyn takeyi ta fito..
     Tana saukowa ta ganta sae tace mata _lfya naganki haka?_ inji momy dan abun ya bata mamaki dan ita dae tasan ba wani abunda ya hada su da dadewa."Ban saniba munafuka"inji umma, ta fada ne a harziqe sannan ta cigaba da cewa _miye jaleel yayi miki zaki zage shi ki kore shi shida gidan uban sa_? Sae momy tace _ni ban zage shi ba illa dae na masa fada dan abunda yyi be dace ba, ina kwance fa a daki naji kukan fadwa shine na fito dan ganin ko meke faruwa kwae sae na ganshi da bulala yana zaneta shine na raba su, yanxu fadwa harta kai na duka da bulala, kuma idan ta mishi abune ba sae ya fada mun ba balle ma bbu abunda ta mishi wae dan...._ bata qarasa ba umma ta cigaba _tayi mishi rashin kunyan sannan kice bata mishi komae ba, to wllhy zan dau mataki akanki keda yar ki_ sannan ta fice ta banko kofar da qarfi wanda yasa fadwa tashi daga baccinta....
   Tana fita tayi side dinta ta samu jaleel na palour kan kujera har yanzu kuka yakeyi ta zauna a gefensa tana lallaminsa _kayi hkuri kaji autana in ta sake maka wani abu ka mata dukan tsiya nina baka wannan izinin kuma idan uwarta ta maka wani abun kazo ka gaya mun_ yace _tou_ yana share hawayen idonsa... tasleem ce ta shigo da sallamarta umma ta ansa sannan ta zauna kan daya daga kujerun palourn ta kalli umma da jaleel sannan tace _umma meyasama autanna ki ne _? Umma tace _wae fadwa tayi mishi rashin kunya danya buge uwarta ta zage shi ta koresa_ Tasleem ta yamutse fuska tace _lallae yaro da gidan ubansa ai da ka mata rashin mutunci_ sae umman tace _barni da ita kwae yanzuma na sameta na kashe mata warning ae_

    Gurin momy kuwa daki ta koma yanda ta taradda fadwa ta tashi amma tana kwance jikinta duk yyi zafi zazzabine ya kamata,haka ta dauketa ta kaita asibiti,bayan wasu yan gwaje2* magunguna aka rubuta musu,  koda likitan ya tambaya wa yyi mata bugu hka sae momy tayi karyan cewa a a scul neh sae kwae yace Allah ya kiyaye gaba amma wannan ae bata kai na duka hka ba,dan Allah a ringa kula momy tace insha Allah sannan tayi godiya suka tafi bayan ya rubuta musu wasu magungunan dan ciwukan jikinta,,bayan sun siya sae suka wuce gida....
   Washegari ya kasance ranar talata neh fadwa bataje scul ba saboda yanayin jikin nata,, around 10:13am sae momy taji sallamar Faiza dama yau tace zata dawo amma momy tayi mamkin ganinta yanxu dan ta mayar saeda yamma zata dawo,ta ansa sallamar gami da jin dadin ganinta a yanxu dan da batazo yanzunba da saedae momy ta fasa zuwa aikinta...
   Bayan sun gaisa sae faiza ke tambyan momy lfya fadwa bata je makaranta ba sae momy ta fada batada lfya sannan ta koro mata duk abubuwan da sukayi ta faruwa bayan tafiyanta daman tasan duk abubuwan dake faruwa a gidan tace _tou Allah ya kauta_ momy tace "ameen" sannan ta tashi shirya dama tayi wanka sannan ta tafi office dinta.....

For comment whatsapp me @ 08102992472
[2:54pm, 12/5/2016] Hamagee馃尫: *KOMAI RINTSI...馃槍*

*By* 馃尫Hamergee馃尫


0鈨�7鈨�
    Koda momy ta tafi hankalin ta kwance yake bata tunanin komai dan tasan indai faiza na nan tou kaman tana nan neh dan zata kula mata da fadwa da gidan kaman tana nan.Bayan momy ta fita faiza ta gyara gidan tsaf duk da dai ba wae datti yyi ba,bayan ta gama sae ta iza girkin rana sannan fadwa ta tashi daga bacci,, wanka tayi mata sannan ta bata abinci taci sae ta bata maganinta da momy ta bari a bata, bayan sun gama around 12:35am  sae suka zauna kallo a palour.Ba laifi jikin fadwa ya danyi sauqi dan har tadi takeyiwa faiza...
    Kamar kullum past two momy ta dawo taci abinci tyi wanka sannan bayan sallan laasar suka shirya suka je kasuwa sayen kayan abinci sannan suka wuce wani babban shoppng mall suka gama siyayyansu suka koma gida.....Washegari fadwa taje scul dan ta samu sauqi ssae,hka rayuwa ta ci gaba musu basu sake samun wata matsala da su umma ba...

  *5 months l8re*....
   Yau ya kasance ranar friday,12noon momy ta taso daga office, tun tashinta take jinta baa daedae ba dauriya kwae takeyi,bayan ta tashi ta dauko fadwa a scul sae suka dawo gida, wanka tayi da qyar ta hado da alwala sae tayi sallah,koda faiza ta kawo mata abinci cewa tayi ta tafida shi kwae bata ciba,, faiza ta tambyeta kou bata jin ddi neh tace mata _ehh_.....Tana nan a kwance a qasa yadda tayi sallahn saeta fara jin kaman ana mitsininta a ciki sae qaruwa kuma yake,, ciwon ciki da baya neh suka sata a gaba lokaci guda _Faizaaa,faizaaaa, faiz......_ bata gama fada ba sae taji ta kasa,, da sauri faiza ta shigo dakin dan dama a saman take dakin fadwa ita kanma bacci takeyi

_______________
   Tana shigo ta fita ganin halinda momyn take ciki  drivern su taje tayi ma magana da sauri ta taimaka ma momy suka shiga motan sannan suka nufi asibiti.Suna isa aka karbesu da gaggawa aka dauko wheel-chair aka tura momy sae labour room yadda ta haifo kyakyawan danta me kama da fadwa..

  For comment whatsapp me @ 08102992472...
[2:54pm, 12/5/2016] Hamagee馃尫: *KOMAI RINTSI....馃槍*

*By*馃尫Hamergee馃尫

0鈨�8鈨nd0鈨�9鈨�
   Haj.Aisha ce keta safa da marwa a ward din daedae nan nurse din da ta karba haihuwar ta fito,tana kallonta ta nufo ta da sauri nurse din ce ta tambayeta _kuna tareda wacce ta haihun neh?_ haj.aisha ta ansa da _eh, ta sauka lfya?_ nurse din tace _lfya klou kuna iya shiga ku ganta a can dakin ma_  dan a lokacin faiza ma ta shigo taje gida dauko kayan baby dana momy da fadwa kamar yadda haj.aisha ta umurceta da tayi...
 Nurse din na tafe suna binta har zuwa dakin ba nisa da inda suke,suna shiga sukaga baby da momy ita kanma bacci neh ya dauketa,faiza ta dauki babyn tana kallo kafin ta miqowa hajiyan momy,,Abba wato mahaifin momy neh ya shigo dakin gami da sallama bayan ya tambyi wata nurse dakin ta nuna mishi,suka ansa bayan ya shigo faiza ta gaida shi ya ansa da faraa sannan ya juya yana yima babyn wasa sae ya juya yana kallon hjiyan yace_kin sama mata wacce zatana kulada ita neh kou kuma zakije da kanki?_ tace _ai da cewa nayi zamu tafi gida kwae da ita inaga kaman zaefi sauqi._  Abba yace _aa ta koma gidanta kwae sae daga baya ta dawo ko bayan anyi suna kafinnan ma mu tattauna da yan iyayen mijin natan_ haj tace! _tou shikenan sae ta koma tunda ga faiza,inyaso sae na ringa dubasu tym to tym_  yace _da  yafi, yanxun an kirasu an sanar da su ta hauhu neh?_ hajya tace _eh,na kira ita matar gidan sun dae na sanarda ita amma bata zo ba har yanxu_ yace _tou ba laifi_ sannan ya fice..
   Bayan sallahn ishai suka tattara kayansu bayan momy ta tashi a bacci sae suka koma gida,momy tayi wanka da taimakon hjya snnan fa'iza tayima bbyn itama.Sanda dare ya soma yi kafinnan hjiyan ta tafi..*hka suka cigaba dayi hjya na zuwa lokaci lokaci tana dubasu faiza kuma na rainon baby kuma tana timakon momy har ran suna,,ana gobe suna gidan wan babansu fadwn suka zo wato Brrs.Khaleed,shi ya rada ma yaron suna.Yaron yasha sunan kakanshi (baban momy),wato Usman sae ana kiransa da khalifa.Ansha suna an watse dangin momy dana baban fadwa duk sunzo,na nesa dana kusa....
    2day ltr..
Alhj Usman da wan baban fadwa da kuma wasu baffanunsa suka zauna sukayi magana kan yanxu kam momy zata iya komawa gida tunda ta gama idda.Fadwa kuma zaa barta gun yan uwanta sae momyn ta tafi babyn,a haka suka tsaida magana sannan kowa ya koma gidansa, momy ta koma gida amma fadwa na gidansu faiza ma ta tafi dan ba abunda zata zaunayi.....
  Da kyar umma ta yarda zata zauna da fadwa dan a cewarta bazata yi raino ba...

    Kar kuji ni shiru da yawa bana jin dadi neh amma in na samu sauqi komi zae canza insha Allah馃檹馃徎

  For comment whatsapp me @ 08102992472 or contact me @ 08091045865
[2:54pm, 12/5/2016] Hamagee馃尫: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁 *KOMAI RINTSI.....* 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯

_Written by_ 馃尫Hama gee鉁嶐煆�

Page 馃敓
    Rayuwar qunci, kadaeci bbu wanda Fadwa bata saba dashi ba a yanxu,, ta sauya yanxu kaman ba itaba baa kulawa da ita kwakwata ko wanka sae dai in tayi niyya tayi da kanta randa batayi wannan tunanin ba kuwa sae dai ta zauna haka dan umma tace ita baza ta iya rainon yar kishiya ba...kullun da datti take zuwa scul dan yanxu sun koma tana nursery2 yayanta jaleel kuma ya shiga js 2....
     Kullum a scul sae haj.faty wato (maman saeema qawar momy) ta bata abun break tareda yi mata dadadan kalamai kan tayi hakuri in ta gama class din da take yanxu zatazo ta dauke ta ta koma gidansu wajen saeema, idan fadwa taji haka sae ta dan ji dadi (abunka ta yarinta) da haka suke rabuwa da ita, idan an tashi kuma fadwa na riga tafiya dake ana riga zuwa daukansu,ranan da tsiyan jaleel ya tashi kuwa cewa yakeyi shi dae ba zae tafi da ita ba saedae akai shi a dawo a dauketa kuma hakan akeyi,infact ya sha yin hakan (ranan da suke tashi tare kenan)...islamiyan su kusa da gida neh wannan tana iya zuwa da kanta.
    Momy fah?
kullum tunanin momy a wane hali fadwa ke ciki? Da tunanin take tashi take kwana (Allah sarki,uwa kenan鈽�),, ranan da haj.faty tazo gun momy neh take fada mata halin da fadwa ke ciki kuma tana yawan yin kuka in sun hadu wae ta kaita kun momynta....
[2:54pm, 12/5/2016] Hamagee馃尫: 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁 *KOMAI RINTSI* 馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯馃崁馃尯

_Written by_ 馃尫Hama gee鉁嶐煆�

No comments:

Post a Comment