Tuesday 23 October 2018

Hausa Novel: Shi Kadai Nake So ( By Beelybadaru )





*SHI KADAI NAKE SO*
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
           ✨✨✨
              ✨✨
                 ✨

✨By Beelybadaru😍✨

_Bismillahir-rahmanir-rahim_

*Wannan littafin nawa qagaggen labari ne banyi don cin xarafin wani ko wata ba, idan yayi dai dai da labarin rayuwarka ka gafarceni, kuma kar wanda ya juya min labarina ta wata siga, wanda yayi hkn na barsa da Allah...*


            ✨1 to 5✨

_I dedicated this page 2 u Ayusher Moh'd, Rabi'at sk msh, Asy khaleel, Wally, Aneelurv(Sweet dota), First lady, Mufeeda Mu'axu, HummyB(Melody), Afma, Yarruma(Sweet momma)._


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

```Kallon juna suke cike da so da qauna, kai da ka gansu xaka tabbatar da cewa su masoyan juna ne na ainihi. Ita ta soma sauke idonta daga kallon da suke ma junansu, sannan ta dago tare da cewa "*Habeeby* ina sonka fiye da yanda nake son kaina, bana tunanin xan iya rayuwa ba tare da kai ba, kaine majinginin rayuwata idan ka matsa rayuwata gaba daya rugujewa xatayi".

Dagowa yayi shima ya kalleta cikin so da qaunarta da suke yawo cikin jinin jikinsa sannan yace "*Habeebty* sonki a cikin jinin jikina yake, soyayyarki wani bangarene mai mahimmanci a rayuwata, cireshi a cikin xuciyata abu ne mai wahalar gaske, ta yaya kike tunanin xan iya rayuwa babu jini a jikina? Ta yaya kike tunanin xan iya rayuwa babu xuciya a jikina? Cire sonki a raina ba abune mai yuwuwa ba, don kuwa idan har aka ce xa'a cireshi ai dai a debe duka jinin jikina domin kuwa sonki a cikin jinin jikina yake yawo".

Lumshe ido ta tayi cike da jin dadin kalamansa, haqiqa sunyi nisa a soyayyar junansu, rabasu abune mai wahalar gaske.

Bude baki tayi da nufin yin magana sai ji tayi an fincikota ta baya, waigawa tayi da sauri don ganin ko waye, gabanta ya fadi ganin Abbanta da tayi tsaye a gabanta fuskarsa daure kamar wanda aka aikoma da saqon mutuwa.

Jikinta ne ya dauki kyarma, durqushewa tayi a gabansa hawaye har sun soma xarya a kumatunta, shima durqushewar yayi cike da jin tsoron abinda Abba xaiyi masu.

Wani wawan mari Abba ya watsa mata, a gigice ta dafe kuncinta don har wasu taurari ta gani shima da hanxari ya dafe kuncinshi don ji yayi kamar shi aka mara don yaji xafin marin har cikin xuciyarshi.

Cikin bacin rai Abba yace "*KHADEEJAH* ni xaki maida qaramin mutum? Ni xaki kunyata? Ke har kin isa in yanke magana a kanki ki bijiremin? To bari kiji in fada maki ko xaki mutu baxaki auri wannan yaron ba auren xumunci xakiyi kamar yanda kowane dan'uwanki yake yi".

Ya waiga ya kalli saurayin da har lokacin bai sauke hannunshi  daga dafe kuncin da yayi ba, yace " Kai kuma ban gargadeka ba akan kar na sake ganinka da diyata ba? Karka kuskura na sake ganinka da ita idan ka bari hakan ta faru......" Yayi kwafa, sannan ya juya ya fara tafiya can ya waigo kuma ya kallesu sannan yace "Ki tabbatar da kin shigo gida cikin secon biyu".

 Da sauri ta miqe ta qarasa gabanshi ta durqusa tare da hade hannayenta biyu guri guda sannan cikin muryar kuka tace " Abbana na roqeka da Allah kayi hkr kayi min rai karka rabani da *AHMAD* wllh shine rayuwata baxan iya auren kowa b in bashi ba, *SHI KADAI NAKE SO* zuciyata tarwatsewa xatayi Abba idan har ka rabani dashi".

Wani dogon tsaki yaja ya tare da yin ball da ita yace "Ah lallai dole xakizo ki tasani ki ri qa gayamin magana n ranki, to bari kiji in gaya miki dolenki ki amshi auren xumunci kamar ynd yan uwanki suka amsa, daga rana irin ta yau bake ba Ahmad kinji na fada miki".

Jin hakan yasa Ahmad yayi saurin qarasowa wajen Abban shima ya durqusa gabanshi tare da cewa " Abba don Allah karka rabani da Khadeejah wllh *ITA KADAI NAKE SO* Abba meyasa kake neman ruguxa mana rayuwarmu, Abba don Allah kayi hkr ka barmu  mu auri junanmu".

Banxan kallo ya watsa mashi sannan ya shige cikin gida. Ahmad har ya fara xubar da hawaye, da sauri Khadeejah tace "Ka daina xubar da Hawayenka Habeeby, xuciyata quna take a duk sanda naga hawayenka na xuba".

Shima kallonta yayi sannan yace " Habeebty kema ki daina xubar da naki hawayen ko kadan bana son ganin hawayen


No comments:

Post a Comment