Showing posts with label Labarai. Show all posts
Showing posts with label Labarai. Show all posts

Thursday 22 November 2018

YA SAYYADI YA YI LALATA DA DALIBARSA A KANO

November 22, 2018 0





YA SAYYADI YA YI LALATA DA DALIBARSA A KANO

Daga Ibrahim Rabiu Kurna

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta yi holin wani Ya Sayyadi wanda wasu iyaye suka dauka don ya karantar da 'ya'yansu su 7 karatun Alqur’ani a gida amma ya yi amfani da wannan damar ya haikewa 'yar karamar su mai shekara 8  a cikin gidan.

Ya Sayyadin mazaunin unguwar Dakata, yana da aure ya ce yarinyar ce take matsowa kusa da shi tace masa za ta yi rubutu sai ya daga ta daga nan dai sai shaidan ya rinjaye shi har ya biya bukatarsa da ita.

Ya amsa laifinsa, inda yace kaddara ce Allah ya kawo masa hakan kuma ba ta taba faruwa akansa ba sai a wannan lokaci, ya nuna nadamar sa da yin da na sani akan abinda ya aikata na haikewa karamar yarinya.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, SP Magaji Musa Majia, ya ja hankalin iyaye da su lura tare da sanin irin malaman da za su dinga dauka domin koyar da 'ya'yan su karatu.

Atiku Zai Sha Kaye A Hannun Buhari Amma Ba Da Ratan Kuri'u Masu Yawa Ba, Inji Shekarau

November 22, 2018 0

ZABEN 2019

Atiku Zai Sha Kaye A Hannun Buhari Amma Ba Da Ratan Kuri'u Masu Yawa Ba, Inji Shekarau

Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Dan takarar Sanata a Kano ta tsakiya a jam'iyyar APC, tsohon gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau ya ce "babu tantama shugaban kasa Muhammadu Buhari zai koma kan kujerarsa a zaben 2019 da izinin Allah.

Mallam Shekarau ya ce zaben da za a yi a badi 2019 ba irin na 2015 bane. Musulmi da Musulmi ne kuma dan arewa ne da dan arewa a tsakanin APC da PDP. Don haka Buhari zai kada Atiku amma ba da irin rinjayen wancan yanayin ba.

Duka wadannan kalamai, Mallam Shekarau ya yi sune a ranar Talatar da ta gabata a garin Badun lokacin da yake zantawa da 'yan jarida, bayan an tashi daga taron kungiyar PSN wato masu harkar magani ta kasa inda suka karrama shi tare da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Ya kara da cewa wannan zaben karo da karo ne, amma Buhari ne mai nasara.

Ana sa rai za a gudanar da zaben shugaban kasa ranar 16 ga Fabrairu 2019, kuma 'yan takara 74 ne za su shiga wannan zabe na shugaban kasa.

Friday 16 November 2018

GARKUWA DA TAGWAYE A ZAMFARA

November 16, 2018 1

GARKUWA DA TAGWAYE A ZAMFARA

Sanata Marafa Ya Bada Gudummawar Naira Milyan Shida

Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto

Sanata Kabiru Marafa ya tallafa da kudi naira milyan shida (N6,000,000) don a biya kudin da za'a sako tagwayen da aka yi garkuwa da su a Zamfara.

Yanzu an samu adadin kudi naira milyan goma sha hudu (N14,000,000) saura naira miliyon daya ya cika naira milyan sha biyar kamar yadda masu garkuwa da tagwayen suka amince cewa sai an biya milyan sha biyar.

 Wannan labarin na tagwayen ya taba hankalin al'ummar kasar nan da wajenta, musamman yadda gwamnatin tarayya da ta Zamfara suka gaza wajen ceto wadannan bayin Allah har saida aka yi karo-karo kafin a bada kudin, abin da ake ganin da wasu manyan jami'an gwamnati ne ko 'ya'yan su da yanzu an biya kudin dan ceto su.