Showing posts with label Labarai. Show all posts
Showing posts with label Labarai. Show all posts

Thursday 22 November 2018

YA SAYYADI YA YI LALATA DA DALIBARSA A KANO

November 22, 2018 0





YA SAYYADI YA YI LALATA DA DALIBARSA A KANO

Daga Ibrahim Rabiu Kurna

Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta yi holin wani Ya Sayyadi wanda wasu iyaye suka dauka don ya karantar da 'ya'yansu su 7 karatun Alqur’ani a gida amma ya yi amfani da wannan damar ya haikewa 'yar karamar su mai shekara 8  a cikin gidan.

Ya Sayyadin mazaunin unguwar Dakata, yana da aure ya ce yarinyar ce take matsowa kusa da shi tace masa za ta yi rubutu sai ya daga ta daga nan dai sai shaidan ya rinjaye shi har ya biya bukatarsa da ita.

Ya amsa laifinsa, inda yace kaddara ce Allah ya kawo masa hakan kuma ba ta taba faruwa akansa ba sai a wannan lokaci, ya nuna nadamar sa da yin da na sani akan abinda ya aikata na haikewa karamar yarinya.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, SP Magaji Musa Majia, ya ja hankalin iyaye da su lura tare da sanin irin malaman da za su dinga dauka domin koyar da 'ya'yan su karatu.

Atiku Zai Sha Kaye A Hannun Buhari Amma Ba Da Ratan Kuri'u Masu Yawa Ba, Inji Shekarau

November 22, 2018 0

ZABEN 2019

Atiku Zai Sha Kaye A Hannun Buhari Amma Ba Da Ratan Kuri'u Masu Yawa Ba, Inji Shekarau

Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Dan takarar Sanata a Kano ta tsakiya a jam'iyyar APC, tsohon gwamnan Kano Mallam Ibrahim Shekarau ya ce "babu tantama shugaban kasa Muhammadu Buhari zai koma kan kujerarsa a zaben 2019 da izinin Allah.

Mallam Shekarau ya ce zaben da za a yi a badi 2019 ba irin na 2015 bane. Musulmi da Musulmi ne kuma dan arewa ne da dan arewa a tsakanin APC da PDP. Don haka Buhari zai kada Atiku amma ba da irin rinjayen wancan yanayin ba.

Duka wadannan kalamai, Mallam Shekarau ya yi sune a ranar Talatar da ta gabata a garin Badun lokacin da yake zantawa da 'yan jarida, bayan an tashi daga taron kungiyar PSN wato masu harkar magani ta kasa inda suka karrama shi tare da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Ya kara da cewa wannan zaben karo da karo ne, amma Buhari ne mai nasara.

Ana sa rai za a gudanar da zaben shugaban kasa ranar 16 ga Fabrairu 2019, kuma 'yan takara 74 ne za su shiga wannan zabe na shugaban kasa.

Friday 16 November 2018

GARKUWA DA TAGWAYE A ZAMFARA

November 16, 2018 1

GARKUWA DA TAGWAYE A ZAMFARA

Sanata Marafa Ya Bada Gudummawar Naira Milyan Shida

Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto

Sanata Kabiru Marafa ya tallafa da kudi naira milyan shida (N6,000,000) don a biya kudin da za'a sako tagwayen da aka yi garkuwa da su a Zamfara.

Yanzu an samu adadin kudi naira milyan goma sha hudu (N14,000,000) saura naira miliyon daya ya cika naira milyan sha biyar kamar yadda masu garkuwa da tagwayen suka amince cewa sai an biya milyan sha biyar.

 Wannan labarin na tagwayen ya taba hankalin al'ummar kasar nan da wajenta, musamman yadda gwamnatin tarayya da ta Zamfara suka gaza wajen ceto wadannan bayin Allah har saida aka yi karo-karo kafin a bada kudin, abin da ake ganin da wasu manyan jami'an gwamnati ne ko 'ya'yan su da yanzu an biya kudin dan ceto su.

Monday 5 November 2018

Kungiyar Kwadago Ta Ta Kasa Ta Janye Batun Yajin Aikin

November 05, 2018 0


DA DUMIDUMINSA

Kungiyar Kwadago Ta Ta Kasa Ta Janye Batun Yajin Aikin Da Ta Kudiri Niyyar Yi A Gobe Talata, Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Amince Za Ta Biya Naira Dubu 30 A Matsayin Mafi Karancin Albashin Ma'aikata.

MAJIYA: Vanguard

ME YA SA BA ZA MU YI WA MASOYA BUHARI UZURI BA?

November 05, 2018 0

ME YA SA BA ZA MU YI WA MASOYA BUHARI UZURI BA?

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

1. ALI NUHU

Miliyoyin masu kallon fina-finan Hausa sun yarda sun amince babu tauraro a kafatanin Kannywood kamar Ali Nuhu Mohammed  Shekara da shekara kusan duk wani shahararren fim din Hausa da ya yi kasuwa ya samu karbuwa a wajen 'yan kallo Ali Nuhu ne a ciki. Su kansu masu shirya fina-finan sun camfa fim idan ba shi ba ya kasuwa.

Tun da aka nada shi Sarkin Kannywood har yanzu shine akan gadon Sarautar an rasa madadinsa. Da dukkan alamu sarautar za ta zama tamkar ta Sarakunan Gargajiya da sai dai ko ya yi murabus ko kuma idan ya mutu a nada wani. Don haka dole ka yi musu uzuri idan suka ce babu sama da shi a harkar FIM.

An musu uzuri saboda an kasa samun dan fim da ya cimma Nasarorin da ya ke da su.

2. RARARA

Tun da Dauda Kahutu Rarara ya fara wakar siyasa ya zama ya yi matsanancin tasirin da ba inda wakarsa ba ta shiga. Kowane dan siyasa burinsa ace Rarara ne ya wake shi. Ya zama sanadiyyar girgiza miliyoyin matasa wajen sauya gwamnati. Zuwa yanzu babu wani mawakin siyasa da za ka ji ana Kace-nace akansa kamar Rarara.

 Masoyansa na kallonsa a matsayin babu mawakin da ya kai shi iya zazzago baituka cikin hikima da salo masu tarin yawa ba tare da gazawa ba. A cewar su ya fi kowane mawakin siyasa suna da daukaka a yanzu.
An Musu uzuri saboda babu mawakin siyasa da ya taka matsayin da ya taka.

3. MUHAMMADU BUHARI

A tarihin siyasar Najeriya babu wani dan siyasa da TALAKA ya nuna zunzurutun so da kauna kamar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Talakawa sun yi kone-kone gami da hargitsa Najeriya saboda zargin an murde masa zabe. Talakawa sun tara masa kudi don ya zama shugaban su.

Talakawa sun mutu saboda murnar ya ci zabe. Talakawa sun sha ruwan kwata, sun zuba ruwa a kasa sun sha, sun yi tafiyar dubban kilomita a kafa saboda da murna. Shine Malaman Addini suka hau Mumbarin wa'azi, Limamai suka hau Mumbarin Juma'a suna fadakar da Talakawa su zabe shi. Sun bugi kirji sun ce babu kamarsa a tsananin farin jini da tasiri a zuciyar Talakawa a yanzu.

Amma an ki yi musu uzuri duk da an kasa kawo wanda ya kai shi.




Uwargidan Gwamnan Bauchi Ta Baiwa Mata 400 Tallafin Kudi

November 05, 2018 0


Uwargidan Gwamnan Bauchi Ta Baiwa Mata 400 Tallafin Kudi

Uwargidan Gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Abubakar ta tallafawa mata 400 a karamar hukumar Azare a karkashin ta na NGO da B-SWEEP.

Wannan shine karo na biyu da mata suke amfana da shirin bada tallafin a karamar hukumar ta Azare. 

A 'yan watannin baya an gudanar da shiri makamancin haka a karamar hukumar Bauchi, inda mata sama da 500 suka amfana da shirin.

Makasudin shirin shine domin tallafawa mata a fadin jihar domin soma gudanar da sana'o'i domin dogaro da kai da kuma tallafawa iyalansu.

An gudanar da shirin ne a garin Azare karkashin shirin na B-WEEP na Uwargidan Gwamna na Bauchi Hajiya Hadiza M.A Abubakar.

Uwargidan ta kuma ziyarci asibitin Azare inda ta tallafawa mata masu juna biyu da sauransu.

Haka kuma uwargidan gwamnan da tawagarta sun ziyarci fadar Sarkin Katagum, Alhaji Umar Muhammad Kabir Umar, inda ta yi masa karin haske kan shirin nata da kuma nasororin da aka samu. 

Daga bisani Sarkin ya yi wa shirin na B-WEEP da uwargidan Gwamnan fatan nasara.

Wasu daga cikin wadanda suka yi wa Uwargidan Gwamnan rakiya a yayin shirin bada tallafin sun hada da matar mataimakin Gwamnan Bauchi, Kwamishiniyar harkokin mata da yara da kuma wasu manyan masu fada a ji.

Haka kuma mataimakin Gwamnan Bauchi, Arch. Audu Sule Katagum da kuma shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Bauchi, Alhaji Tijjani Mohammed Aliyu da sauransu da dama na daga cikin wadanda suka halarci taron.

RARIYA ta samo labarin ne daga mai taimakawa Gwamnan Bauchi kan harkokin sadarwa, Shamsuddeen Lukman Abubakar.






Thursday 1 November 2018

Mutuwar Janar Idris Alkali Abin Dubawane

November 01, 2018 0



DUNIYA TA SAN DA WANNAN!

Daga Datti Assalafy

Haka kawai ‘yan ta’addan berom ba zasu tare motar Janar Idris Alkali bayan ya fada musu cewa shi babban hafshin soji ne mai mukamin Janar amma basuji tsoro ba suka kamashi suka kashe, dole akwai wani abu wanda binciken kwakwaf ne kadai zai bayyana, domin mun samu bayanai daga wajen ‘yan uwanshi na jini cewa Janar Idris ya bada wasu shawarwari kwanakin da basu wuce biyu ba sai wannan abin ya faru da shi.

Hakika ‘yan ta’addan berom sun taba zuciyarmu, sun yiwa ‘dan uwanmu musulmi mafi munin wulakancin kisa, ku kashe mutum ko bunne sannan ku sake tonewa ku jefa a rijiya, wani irin wulakanci ne wannan?
Jama’a zaku iya tuna wani screen short da na daura muku kwanakin baya?, inda wani ‘dan ta’addan berom ya tabbatar mana da cewa Janar Idris Alkali ya mutu, kuma mutuwar wulakanci, idan kun tuna na saka muku har da hotonshi.

Rundinar sojin Nigeria tace bayan sun jefa gawarshi a rijiya sai suka jefa manyan duwatsu masu nauyin gaske a kan gawarshi, saboda tsabagen wulakanci da kasancersu cikakkun tsinannu bakaken kafurai maguzawa ‘yan ta’adda.

Na saurari jawabin da Birgediya Janar Umar Muhammad yayi bayan sun fito da gawar Janar Idris Alkali daga cikin rijiyar, yana alwashin cewa duk wanda yake da hannu a kisan Janar Idris Alkali komin gatansu da duk wadanda zasu tsaya musu wallahi sai sun fuskanci hukunci.


To abinda kawai za’a mana ya kwantar mana da hankali shine a shafe garin Dura-Du daga tarihi, a rusa garin, a mayar da garin sansanin horar da jami’an tsaron Nigeria, sannan a sakawa sansanin sunan Manjo Janar Idris Alkali domin ya zama abin tunawa har zuwa ranar da Allah (SWT) Zai tashi duniyar.

Jiya babban yayan marigayi Janar Idris Alkali Air Commodore Ibrahim Alkali (Mairitaya) ya bada sanarwan cewa za’a gabatar da sallar “Salatul Ghaa’ib” wa Marigayi Janar Idris Alkali bayan sallar Azahar a babban masallacin juma’a na garin Potiskum dake fadar Masarautar Fika, bayan sun samu tabbaci daga rundinar sojin Nigeria cewa an gano gawarsa, amma kafin lokacin sai aka dage sallar.

Salatul Ghaa’ib wata irin sallar jana’iza ce da ake gabatar wa duk wani musulmi da ya mutu amma ba’a samu gawarsa ba, ko kuma gawarsa na hannun wadanda ba musulmi ba ana iya masa Salatul Ghaa’ib.
Lokacin da Sarkin Habasha Sarki Annajjashi ya rasu, kuma ya rasu a hannun jama’arshi da ba musulmi ba, sai Annabi (SAW) ya gabatar masa da Salatul Ghaa’ib.

Kamar yadda rundinar sojin Nigeria ta fitar da sanarwa tace yanzu haka gawar Janar Idris Alkali tana babban asibin shiyya ta uku na rundinar sojin Nigeria dake birnin Jos, ana jiran umarni na gaba daga hedkwatar tsaron sojin Nigeria dake Abuja kafin wani abu ya biyo baya.

A hoto na farko Janar Idris Alkali ne tare da mahaifiyarshi Baaba Halima ‘yar shekara casa’in da uku, itace wacce yafi so da kauna a duniya, ance ko yaje gida hutu baya kwana a gidansa sai a gidansu na gado kuma a dakin mahaifiyasar suke kwana tare yana debe mata kewa yana mata hidima, jama’a kuna tunanin Allah zai kyale mutanen da suka raba irin wannan soyayya da ladabi dake tsakanin uwa da ‘danta? wallahi su kwana da shirin cewa zasuga mummunan sakamako tun daga nan duniya.

Yaa Allah Ka jikan Janar Idris Alkali
Allah Ka sa ya dace da mutuwar shahada Amin.

Wednesday 31 October 2018

An Gano Gawar Manjo Janar Alkali A Tsohuwar Rijiya

October 31, 2018 0




An Gano Gawar Manjo Janar Alkali A Tsohuwar Rijiya

Rundunar sojojin Najeriya sun tabbatar da cewa an gano gawar Marigayi Manjo Janar Idris Alkali a wata tsohuwar rijiya a wani anguwa da ake kira Guchwet da ke Shen a karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato.


Shugaban masu binciken na Sojoji Umar Mohammed ya tabbatar da ganin gawar sojar da ya bace tun a ranar 3 ga watan Satumba 2018 a kan hanyarsa ta zuwa Bauchi daga Abuja a Jos.








Dandazon Turawan Da Suka Ziyarci Saudiyya Gudanar Da Umrah Bayan Sun Musulunta

October 31, 2018 0

Dandazon Turawan Da Suka Ziyarci Saudiyya Kenan Domin Gudanar Da Umrah Bayan Sun Musulunta 

Tuesday 30 October 2018

Dole A Daina Kashe-Kashe A Kasar Nan –Buhari

October 30, 2018 0


Shugaban kasa Buhari ya ce dole wannan kashe-kashen na rashin hankali ya tsaya, musamman a jihar Kaduna da take fama da rikicin kabilanci da na addini, Buhari ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar sun kamu duk masu hannu a aikata wannan ta’asar ta kisan mutane ba gaira ba dalili, domin su fuskanci shara’a.

Buharin ya furta wadannan kalaman ne a daidai lokacin da ya ziyarci jihar Kaduna don gane wa idon shi irin barnar da rikicin ya yi.


‘Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar ta hukunta duk wanda ta samu da hannu a wannan rikicin, ba zamu bar masu laifi su dinga walwala ba, don haka duk mai hannu a wannan rikicin ya tabbatar da zai fuskanci hukunci.’ inji Buhari

Buhari ya kara da cewa, ina rokon dukkan al’ummar jihar Kaduna, da su zauna lafiya da juna, ba za mu lamunci tashin hankali ba da kashe-kashe na ba gaira ba dalili, sannan mun yaba da kokarin gwamnatin jihar wajen dakile rikicin.

Sunday 28 October 2018

Dalibi Dan JSS 3 Ya Dirkawa Wata ‘Yar Bauta Kasa Cikin Shege

October 28, 2018 2






Wani dalibi a wata karamar makarantar sakandire da aka sakaya sunanta a jihar Abiya ya dirkawa wata budurwa mai yiwa kasa hidama karkashin NYSC cikin shege.

Lamarin dai ya janyo cece kuce a makarantar ta yadda akai mai yiwa kasa hidamar har ya bari dan aji uku na karamar sakandire yayi kwance kwance ya dirka mata ciki.


Wasu da dama na ganin duba da yadda ‘yar yiwa kasa hidimar ta baiwa dalibin tazarar shekaru bai kamata ace ya bari hakan ya auku tsakaninsu ba, yayin da wasu ke tunanin ko barazana dalibin ya yiwa budurwa.

Ana dai cigaba da gudanar da bincike domin gano bakin zaren matsalar da yadda za a warware ta.


Source@ Arewablog.Com

Thursday 25 October 2018

An Sace Wasu Tagwaye A Jihar Zamfara

October 25, 2018 0



An Sace Wasu Tagwaye A Jihar Zamfara
Daga M Badaruddeen Bature

yanzu masu satar Shanu Mutane suke sata a jiharmu. Inda aka sace wasu tagwaye Hassana da Husaina a yankin Daura dake karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Wannan jarabawar ta sace-sace da kashe-kashe dake adabar mu Allah ka kawo mana karshen ta a jihar mu da kasar mu baki daya.

Source@ Arewablog.Com