Monday 5 November 2018

Uwargidan Gwamnan Bauchi Ta Baiwa Mata 400 Tallafin Kudi



Uwargidan Gwamnan Bauchi Ta Baiwa Mata 400 Tallafin Kudi

Uwargidan Gwamnan jihar Bauchi, Hajiya Hadiza Abubakar ta tallafawa mata 400 a karamar hukumar Azare a karkashin ta na NGO da B-SWEEP.

Wannan shine karo na biyu da mata suke amfana da shirin bada tallafin a karamar hukumar ta Azare. 

A 'yan watannin baya an gudanar da shiri makamancin haka a karamar hukumar Bauchi, inda mata sama da 500 suka amfana da shirin.

Makasudin shirin shine domin tallafawa mata a fadin jihar domin soma gudanar da sana'o'i domin dogaro da kai da kuma tallafawa iyalansu.

An gudanar da shirin ne a garin Azare karkashin shirin na B-WEEP na Uwargidan Gwamna na Bauchi Hajiya Hadiza M.A Abubakar.

Uwargidan ta kuma ziyarci asibitin Azare inda ta tallafawa mata masu juna biyu da sauransu.

Haka kuma uwargidan gwamnan da tawagarta sun ziyarci fadar Sarkin Katagum, Alhaji Umar Muhammad Kabir Umar, inda ta yi masa karin haske kan shirin nata da kuma nasororin da aka samu. 

Daga bisani Sarkin ya yi wa shirin na B-WEEP da uwargidan Gwamnan fatan nasara.

Wasu daga cikin wadanda suka yi wa Uwargidan Gwamnan rakiya a yayin shirin bada tallafin sun hada da matar mataimakin Gwamnan Bauchi, Kwamishiniyar harkokin mata da yara da kuma wasu manyan masu fada a ji.

Haka kuma mataimakin Gwamnan Bauchi, Arch. Audu Sule Katagum da kuma shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Bauchi, Alhaji Tijjani Mohammed Aliyu da sauransu da dama na daga cikin wadanda suka halarci taron.

RARIYA ta samo labarin ne daga mai taimakawa Gwamnan Bauchi kan harkokin sadarwa, Shamsuddeen Lukman Abubakar.






No comments:

Post a Comment