Monday 17 September 2018

Hausa Novel: Rayuwar Najwa ( By Ummu Basheer )

September 17, 2018 0

🌹 *RAYUWAR NAJWA*🌹

                 🌹

     {  *Labari mai cike da tausayi da k'auna* }



   *NA*
*UMMU BASHEER*


® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
    (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader's📚)_



*PAGE* *1*~*2*







*Garin* yayi duhu sosai kasancewar hadari ya had'u ga wani irin iska mai k'arfi da akeyi, wata kyakyawar yarinya na hango sai sauri ta keyi sai dai tana tafiya ne tana d'ingisawa, burin ta d'aya shine ta isa gida kafin ruwan sama ya sauko, cikin ikon Allah har ta isa gida ruwan bai sauko ba. tana shiga  sai ga *INNA* nan ina ta hau ta da masifa kamar zata cinye ta d'anye, wannan yarinyan sai kuka ta keyi kawai. 

Cikin kuka tace" Dan Allah kiyi hak'uri INNA wallahi yau banyi ciniki ba"

Cikin masifa Inna tace" Yau naga y'ar banza kina nufin yau ma kinyi min kwantai da Awara, to wallahi ba zai yiwu ba"

Nan Inna ta d'auko wani k'aton ice tayi kan yarinyan nan da shi, ganin haka yasa yarinyan ta ruga wani d'an d'aki da gudu tana d'ingisawa nan Inna ta bita ta fara dukan ta da wannan icen, Allah sarki yarinyan sai ihu ta keyi. dan kanta Inna ta gaji da dukan ta ta k'yale ta. 

Haka yarinyan nan mai suna *UMMI* tayi ta kuka dan duktaji ciwo a jikin ta, a haka har tayi barci.


Washegari da safe da missalin k'arfe shida Ummi na kwance tana barci sai ji tayi an watsa mata ruwa. a firgice ta tashi,Inna ta gani rik'e da bokiti tana cewa" Uban wa zaiyi miki aiki kin kwanta sai barci kike ni tashi kije ki d'ebo ruwa kuma kiyo icce yanzun nan"

Tana karkarwan sanyi ta tashi ta d'auki bokiti ta nufa rafi nan ta d'ebo ruwa sannan tayo icce,bayan nan tace ma Inna" na gama"

Inna dake gaban murhu tana suyan k'osai tace" to d'auki bokitin koko ki tafi talla"

Tsayawa tayi ba tare da ta d'auka ba nan Inna tace" mene ne kin wani tsaya min a kai?"

Cikin rawar baki tace" Dan Allah Inna yunwa nake ji"

Da masifa tace" to maya in ban baki ba cinye ni zakiyi" nan ta bata wani koko na jiya har yayi tsami, 

Da sauri Ummi ta karb'a hannun ta na rawa tsabar yunwa nan ta hau sha tana gama shanyewa sai amai dan rabon ta da abinci tun shekaran jiya. tana gamawa ta wanke bakin ta sannan ta d'auki tallan ta fita tana d'ingisawa.

Ba ita ta dawo ba sai wurin sha biyu na rana dan takan jima ba'a siya nata ba. tana shigowa Inna ta hau ta da masifa sannan ta bata alallen gwangwani guda d'aya taci. tana gamawa ta shiga d'akin da take kwana wanda ba komai sai buhun kayan ta dan ko siminti babu a d'akin sai k'asa, nan ta shirya cikin riga da wando da farin hijab na makaranta. 

Tana fitowa Inna tace" ke ke tsaya ba inda zaki sai kinyi wanke-wanke wato ke mai son karatu ko to wuce maza ki cire kayan"

Cikin hawaye tace" Inna kiyi hak'uri inje wallahi nayi lati kuma malamin zai min duka"

Wani rangwashi tayi mata a kai mai shegen zafi da sauri Ummi ta aje jakan buhun ta ta fara wanke-wanken.

Wani mutum ne ya fito daga d'akin shi yace" yau naga y'ar banza uban mai ya hana ki aikin tuntuni wai ke a dole mai son makaranta "

Inna tace" Ashe kana jina da ita?"

Yace" Eh ai ni wallahi yaya Auwalu ya cuce ni da ya tafiya bar min wannan abar"

Ita dai Ummi na jin su tayi shiru kawai.

Bayan kwana biyu Ummi na cikin yin tatan kamu sai ga wata yarinya wace ba zata wuce sa'ar Ummi ba. ta watsa mata wasu tsoman kaya tace" ke wanke min kaya na dan biki zani anjima saura kuma kar su fita da kyau haha yarinya zan lakad'a miki na jaki wallahi"

 "Uban wa zaiyi miki wanki?" wani saurayi ya fad'a haka yayin da ya shigo gidan.

Turo baki tayi wanda yaji jambaki har ya wuce bakin tace" *YUSUFA* kana takura min fa"

Da gudu ya bita nan ta shige d'akin Inna tana ihu ai da sauri ina ta dakatar da shi ta fito tsakar gida tana cewa" kai wani irin wawa ne har sai yaushe zaka bar goyon bayan yarinyan nan?"

Cikin zuciya yace" ba zan daina ba Inna dan ni banga abin da tayi muku ba da baku son ta"

Inna tace"Eh d'in ba mu son ta ka fita a ido na fa Yusufa karka manta da kai da *LANTANA* uwa d'aya uba d'aya kuke amma sai ka so wancan matsiyaciyar to ka kiyaye ni"

Cikin haushi ya kalla wanda aka kira Lantana yace" ni dai da ita da *UMMINA* na d'auke su k'anne nane ba wani banbanci"

Habawa ai nan ran Inna ya b'aci ta shiga massifa tana zagin Ummi shi dai Yusufa fita yayi a gidan. Ummi ba abin da take sai share hawaye.